Ta Bukaci Alumma da su yi masa adduar samun lafiya.
Followers
Saturday, March 28, 2020
Yanzu Yanzu: An gano Gwamnan Kaduna El-rufai na dauke da cutar Corona
Shafin kafar Sadarwa na twitter na matar Gwamanan be yabbana haka da yammacin nan, tace tini Gwamnan ya killace kansa duk da cewa be Fara nuna wata alama ta mash cutar ba.
Thursday, March 26, 2020
An sake samun mai dauke da cutar Corona virus a jihar Bauchi.
Kwamishinan lafiya na Jihar Bauchi Dr Aliyu Mohammad Maigoro ne bayyana hakan ga manema labarai a yau Alhamis.
Wannan daya ne daga cikin mutane 48 wadanda suka fi shiga hadarin kamuwa da cutar sakamakon yin mu'amala da mutum na farko mai dauke da cutar a jihar, wato gwamnan jihar Bala Mohammad.
Kwamishinan bai Bayyana ko wanene ( ko kuma ko wacece) mai dauke da cutar ba, sai da bayyana cewa wani Abokin ( Ko kuma kawar) Gwamnan Bauchi Bala Mohammad ne, kuma dan ( KO yar) shekara sittin da biyu ce (ne).
Yace tini a killace me dauke da cutar, kuma Ana bashi kulawa, sannan yaja hankalin mutanen jahar da su cigaba da bawa Gwamnatin jihar hadin kai wajen yaki da cutar.
Tuesday, March 24, 2020
CUTAR CORONA: SHIN DA GASKE SINADARIN CHLOROQUINE YANA MAGANINTA?
Tun bayan da aka samu labarin rahoto na farko na billar cutar corona a kasar man mutane da yawa suka Shiva cikin halin dimuwa DA tashin hankali, karin samun rahottanin bullar cutar a wasu sassa na kasar bayan jihar Lagos da cutar ta Fara bulla a sanadiyar wani mutumin kasar Italiya ya Kara ta'azzara tsoro DA fargaba DA ke cikin zukatan mutane.
kwatsam kuma sai aka samu labarin dake nuna cewa sinadarin chloroquine yana maganin wannan cuta, Tun daga nan ake ta samun turruruwar mutane a shagunan saida magunguna domain siyan wannan magani da niyyar yin Riga kafi.
Abinda ya kamata mutane su fahimta shine illar daukar matakin kare ba tare da samun sahalewa daga masana lafiya ba a wadansu lokutan yakan fi ita cutar da ake kokarin kare kai daga ita din, Dan haka duk da cewa an tabbatar da cewa chloroquine yana maganin kwayar cutar corona hakan ba wai yana nufin cewa za'a iya amfani dashi wajen yin rigakafi bane.
Riga kafin cutar corona, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya take ta kara jaddaddawa sune kamar haka:
1- Yawan wanke hannewa da ruwa da sabulu
2- Yin amfani da sinadarin wanke hannu mai sinadarin kashe kwayoyin cuta ( Hand sanitizer)
3- Kauracewa gurin me cunkosan mutane
4- Yin baya-baya da mutanen da aka suna tari KO attishawa
5- Yin kasan cewa cikin tsafta a ko da yaushe.
Shi kuwa maganin chloroquine wadanda aka tabbatar da cewa sun kamu da wannan cuta ne kadai zai yiwa amfani, kuma masana kiwon lafiya su suka San irin yadda za'a yi amfani dashi don maganin wannan cuta.
Shan maganin chloroquine fiye da kima Nada wadansu hadarrarrrukan da zai iya haifarwa, kamar makantar da mutum da sauransu, dan haka yakamata mutane su kiyayye.
Subscribe to:
Posts (Atom)