An sake samun mai dauke da cutar Corona virus a jihar Bauchi.
Kwamishinan lafiya na Jihar Bauchi Dr Aliyu Mohammad Maigoro ne bayyana hakan ga manema labarai a yau Alhamis.
Wannan daya ne daga cikin mutane 48 wadanda suka fi shiga hadarin kamuwa da cutar sakamakon yin mu'amala da mutum na farko mai dauke da cutar a jihar, wato gwamnan jihar Bala Mohammad.
Kwamishinan bai Bayyana ko wanene ( ko kuma ko wacece) mai dauke da cutar ba, sai da bayyana cewa wani Abokin ( Ko kuma kawar) Gwamnan Bauchi Bala Mohammad ne, kuma dan ( KO yar) shekara sittin da biyu ce (ne).
Yace tini a killace me dauke da cutar, kuma Ana bashi kulawa, sannan yaja hankalin mutanen jahar da su cigaba da bawa Gwamnatin jihar hadin kai wajen yaki da cutar.
No comments:
Post a Comment