Hukumar tallafawa matasa ta N-power ta ayyana cewa a ranar 26 ga watan nan da muke ciki zata bude shafinta na dibar ma'aikata a rukunin C, dan haka ga wadansu ka'idoji da yakamata abi, dan cike takardar neman aikin ba tare da samun wata matsala.
1. Idan mutum ya canza sunansa, to lallai a wajen cikewa yayi amfani da sunan da yake jikin takardunsa da BVN dinsa, ko da kuwa ba shine sabon sunan da ya canja ba.
2. Idan da yiwuwa kayi kokari ka cike da kanka. Karka bawa masu aiki a wuraren cikewar saboda gudun samun kuskure a wajen rubuta sunaye da sauransu. Idan kuma ya zama dole sune zasu cike maka, to ya kasance kana ganin dukkanin abubuwan da suke rubutawa yayin cikewar.
3. Ka duba ka sake dubawa sosai bayan ka gama cikewa kafin ka tura.
4. Ka tabbata lambar asusun bankin da zakai amfani da ita tana aiki kuma tana da alaka da lambarka ta BVN.
5. Ka tabbata sunan da zaka nemi aikin dashi suna ne Wanda yayi daidai da sunan da yake account dinka na banki, Dan haka idan misali a takardunka kana amfani da suna uku, amma asusunka na banki kuma sunaye biyu, to kayi amfanin da suna biyun ko akasin haka.
7. Karka canza yanayin rubutun sunanka da yadda yake account da sauran takardunka, misali idan sunan account da sauran takardunka 'Muhammad' ne, karka canza ka maida shi 'Mohammed'.
8. Karkai amfani da alamar mallaka ( ' ) a sunanka, misali karka rubuta Mu'azu, sai dai Muazu, ko kuma Is'haq, sai dai Ishaq da sauransu.
9. Karkai amfani da takaitawa wajen rubuta sunanka, misali idan sunanka Musa Abdullahi Sani karka rubuta Musa A Sani, da sauransu.
9. Karka amfani da alamomi wajen rubuta sunanka, misali karka rubuta Abdulrrazak karka rubuta Abdul-rrazak.
Shafin Kimiyya da Fasaha zai cigaba da kawo muku hanyoyin wayar dakai akan Neman aikin na N-power.
No comments:
Post a Comment