Coronavirus ta kashe likita a jihar KatsinaWallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wani likita a Daura da ke jihar Katsinan Najeriya ya mutu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus, bayan ya ziyarci jihohin Kogi da Lagos. Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari ya sanar da mutuwarsa bayan an yi gwajin samfurin jininsa a birnin Abuja wanda ya tabbatar cewa cutar ta coronavirus ta kashe shi.
Aminu Bello Masari kan mutuwar likita a Daura bayan fama da coronavirus .
Masari ya ce, tuni suka tashi tawagar likitoci zuwa garin Daura domin diddigin mutanen da likitan ya yi hulda da su da zummar yi musu gwaji da kuma killace su saboda fargabar cewa, su ma sun kamu da wannan annoba.
Mun Kwafo daga shagin rfi
Hausa
No comments:
Post a Comment