Cutar Corona: Masana kimiyya sun gano maganin da yake kashe cutar a cikin awa 48
Masana kimiyya a kasar Australia sunce sun gano wani magani da yake kashe cutar acikin awa 48, kamar yadda jaridar daily mail ta rawaito.
Maganin mai suna ivermectin, asali Ana amfani dashi wajen maganin kwarkwatar kai ne, kuma akwai shi a KO Ina a fadin duniya.
Masu bincike a jami'ar monash sun gano cewa shan kwayar maganin na ivermectin yana iya kashe kwayar cutar ta corona daga jikin kwayar halittar Dan Adam.
Se dai har yanzu ba'a yi gwajin kwayar maganin a jikin Dan Adam ba.
Masana kimiyyar sunce Abu na gaba shine gano yadda za'ai amfani dashi ga dan Adam wajen maganin cutar ta corona
No comments:
Post a Comment