Followers

Monday, April 6, 2020

Shin da gaske ne shan ruwan dumi ko yin sirace da ruwan zafi na maganin coronavirus?

Shin da gaske ne shan ruwan dumi ko yin sirace da ruwan zafi na maganin coronavirus?

Dakta Nasir Sani-Gwarzo wani fitacce kan harkar lafiya a Najeriya, ya ce yin sirace da ruwan zafi ba ya hana kamuwa da coronavirus amma zai iya taimakawa wajen jika makogwaro.

"Ita coronavirus cuta ce da take yaduwa ta hanci ko baki sai ta gangara makogwaro inda za tai ta hayayyafa har ta shiga huhu" a cewarsa.

Dakta Sani-Gwarzo ya ce idan ana yawan yin sirace, makogwaro zai zama a wanke ba tare da wata majina ba kuma wannan na iya taimakawa wajen hana cutar yaduwa, amma yin siracen ba ya maganin cutar.

Haka kuma shan ruwan dumi na taimakawa makogwaro wajen tsaftace shi da wanke shi yadda ya kamata ko da mutum ba ya dauke da wata cuta, amma Dakta Sani-Gwarzo ya ce ''wannan ba shi zai hana kamuwa da cutar ba kuma ba zai yi maganin cutar ba ga wanda ya kamu"

No comments:

Post a Comment