Followers

Wednesday, October 13, 2021

YAU ZA'A CI GABA DA SHARI'AR ABDULJABBAR GABA-GADI

A yayin zaman na yau dai ana saran shehin Malamin zai zo da littattafai gaban kotu domin ya kare kanshi, abinda ya kasa yi yayin mukabalar da Gwamnatin Kano ta shirya tsakaninsa da wasu daga cikin malaman Jihar.

Shin kuna Ganin malamin zai iya yin hakan a gaban kotu kuwa?

Thursday, September 16, 2021

YADDA RAHAMA SADAU TA BAWA MUTANE MAMAKI A KASAR INDIA

Jarumar Film din Kannywood ta bawa mutane mamaki bayan da aka hotunan ta a kasar Indiya yayin shirin daukar wani film mai suna Guda hafeez.

Monday, September 13, 2021

YANZU-YANZU: SAKAMAKON GWAJIN KWAKWALWAR ABDULJABBAR


Idan Za'iya tunawa kimanin kwani goma sha uku da suka wuce ne aka gurfanar da Malamin nan da ake ake zargi da kalaman batanci ga Manzo (S.A.W) wato Mallam Abduljabbar Nasiru Kabara a gaban kotu a karo.

Sai dai yayi zaman Alkali yayiwa malamin tambaya akan tuhume-tuhumen da ake masa, sai dai shehin Malamin yayi gum da bakinsa bai bada amsa ba. Wanda hakan yasanya Alkalin bada umarnin aje a gwada lafiyar kwalkwalwarsa a asibitin lafiya na Dawanau.

Ya zuwa yanzu dai ba'a bayyana sakamakon binciken ba.

Monday, August 30, 2021

ZAFAFAN HOTUNAN HADIZA GABON MASU DAUKAR HANKALI

YANZU-YANZU: AKWAI YIWUWAR ASUU ZASU TAFI YAJIN AIKI

Jawabin hakan na fitowa ne daga shafin kungiyara ta ASUU na kafar Facebook inda suka wallafa bayani da yake cewa Gwamnati taki saurarensu, jami'an Gwamnati ma sun dena saurarensu, Bama sa daga wayoyinsu. Sukace ya kamata yan Nigeria sun fada Gwamnati tayi abinda tayi alkawarin yi.

Suka ce "mun sanya hannu a yarjejeniya kuma ko a watan may mun cimma matsaya, amma gashi har yanzu a watan August ba abinda aka aiwatar, yanzu hakan yayi daidai? Mun basu zuwa karshen watan August bayan wannan lokacin zamu fara daukar matakai"