Followers

Tuesday, April 7, 2020

Corona Virus Ta kashe mutum na farko a jihar Katsina

Coronavirus ta kashe likita a jihar KatsinaWallafawa ranar: Chanzawa ranar: 

Wani likita a Daura da ke jihar Katsinan Najeriya ya mutu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus, bayan ya ziyarci jihohin Kogi da Lagos. Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari ya sanar da mutuwarsa bayan an yi gwajin samfurin jininsa a birnin Abuja wanda ya tabbatar cewa cutar ta coronavirus ta kashe shi.
Aminu Bello Masari kan mutuwar likita a Daura bayan fama da coronavirus .
Masari ya ce, tuni suka  tashi tawagar likitoci zuwa garin Daura domin diddigin mutanen da likitan ya yi hulda da su da zummar yi musu gwaji da kuma killace su saboda fargabar cewa, su ma sun kamu da wannan annoba.
Ana iya cewa wannan ne karo na farko da cutar coronavirus ke kisa a Jihar Katsina da ke Najeriya.

Mun Kwafo daga shagin rfi
Hausa

Da Dumi-Dumi: An Gano maganin kwayar Cutar Corona

<\head>
Cutar Corona:   Masana kimiyya sun gano maganin da yake kashe cutar a cikin awa 48

Masana kimiyya a kasar Australia sunce sun gano wani magani da yake kashe cutar acikin awa 48, kamar yadda jaridar daily mail ta rawaito.

Maganin mai suna ivermectin, asali Ana amfani dashi wajen maganin kwarkwatar kai ne, kuma akwai shi a KO Ina a fadin duniya.
Masu bincike a jami'ar monash sun gano cewa shan kwayar maganin na ivermectin yana iya kashe kwayar cutar ta corona daga jikin kwayar halittar Dan Adam.

Se dai har yanzu ba'a yi gwajin kwayar maganin a jikin Dan Adam ba.
Masana kimiyyar sunce Abu na gaba shine gano yadda za'ai amfani dashi ga dan Adam wajen maganin cutar ta corona

Monday, April 6, 2020

Shin da gaske ne shan ruwan dumi ko yin sirace da ruwan zafi na maganin coronavirus?

Shin da gaske ne shan ruwan dumi ko yin sirace da ruwan zafi na maganin coronavirus?

Dakta Nasir Sani-Gwarzo wani fitacce kan harkar lafiya a Najeriya, ya ce yin sirace da ruwan zafi ba ya hana kamuwa da coronavirus amma zai iya taimakawa wajen jika makogwaro.

"Ita coronavirus cuta ce da take yaduwa ta hanci ko baki sai ta gangara makogwaro inda za tai ta hayayyafa har ta shiga huhu" a cewarsa.

Dakta Sani-Gwarzo ya ce idan ana yawan yin sirace, makogwaro zai zama a wanke ba tare da wata majina ba kuma wannan na iya taimakawa wajen hana cutar yaduwa, amma yin siracen ba ya maganin cutar.

Haka kuma shan ruwan dumi na taimakawa makogwaro wajen tsaftace shi da wanke shi yadda ya kamata ko da mutum ba ya dauke da wata cuta, amma Dakta Sani-Gwarzo ya ce ''wannan ba shi zai hana kamuwa da cutar ba kuma ba zai yi maganin cutar ba ga wanda ya kamu"