Followers

Sunday, June 28, 2020

YADDA ZAKA CIKE TAKARDAR NEMAN AIKIN N-POWER BA TARE DA KUSA-KURAI BA

Hukumar tallafawa matasa ta N-power ta ayyana cewa a ranar 26 ga watan nan da muke ciki zata bude shafinta na dibar ma'aikata a rukunin C, dan haka ga wadansu ka'idoji da yakamata abi, dan cike takardar neman aikin ba tare da samun wata matsala.

1. Idan mutum ya canza sunansa, to lallai a wajen cikewa yayi amfani da sunan da yake jikin takardunsa da BVN dinsa, ko da kuwa ba shine sabon sunan da ya canja ba.
2. Idan da yiwuwa kayi kokari ka cike da kanka. Karka bawa masu aiki a wuraren cikewar saboda gudun samun kuskure a wajen rubuta sunaye da sauransu. Idan kuma ya zama dole sune zasu cike maka, to ya kasance kana ganin dukkanin abubuwan da suke rubutawa yayin cikewar.
3.  Ka duba ka sake dubawa sosai bayan ka gama cikewa kafin ka tura.
4. Ka tabbata lambar asusun bankin da zakai amfani da ita tana aiki kuma tana da alaka da lambarka ta BVN.
5. Ka tabbata sunan da zaka nemi aikin dashi suna ne Wanda yayi daidai da sunan da yake account dinka na banki, Dan haka idan misali a takardunka kana amfani da suna uku, amma asusunka na banki kuma sunaye biyu, to kayi amfanin da suna biyun ko akasin haka.
7. Karka canza yanayin rubutun sunanka da yadda yake account da sauran takardunka, misali idan sunan account da sauran takardunka 'Muhammad' ne, karka canza ka maida shi 'Mohammed'.
8. Karkai amfani da alamar mallaka ( ' ) a sunanka, misali karka rubuta Mu'azu, sai dai Muazu, ko kuma Is'haq, sai dai Ishaq da sauransu.
9. Karkai amfani da takaitawa wajen rubuta sunanka, misali idan sunanka Musa Abdullahi Sani karka rubuta Musa A Sani, da sauransu.
9. Karka amfani da alamomi wajen rubuta sunanka, misali karka rubuta Abdulrrazak karka rubuta Abdul-rrazak.

Shafin Kimiyya da Fasaha zai cigaba da kawo muku hanyoyin wayar dakai akan Neman aikin na N-power.

Tuesday, April 7, 2020

Corona Virus Ta kashe mutum na farko a jihar Katsina

Coronavirus ta kashe likita a jihar KatsinaWallafawa ranar: Chanzawa ranar: 

Wani likita a Daura da ke jihar Katsinan Najeriya ya mutu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus, bayan ya ziyarci jihohin Kogi da Lagos. Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari ya sanar da mutuwarsa bayan an yi gwajin samfurin jininsa a birnin Abuja wanda ya tabbatar cewa cutar ta coronavirus ta kashe shi.
Aminu Bello Masari kan mutuwar likita a Daura bayan fama da coronavirus .
Masari ya ce, tuni suka  tashi tawagar likitoci zuwa garin Daura domin diddigin mutanen da likitan ya yi hulda da su da zummar yi musu gwaji da kuma killace su saboda fargabar cewa, su ma sun kamu da wannan annoba.
Ana iya cewa wannan ne karo na farko da cutar coronavirus ke kisa a Jihar Katsina da ke Najeriya.

Mun Kwafo daga shagin rfi
Hausa

Da Dumi-Dumi: An Gano maganin kwayar Cutar Corona

<\head>
Cutar Corona:   Masana kimiyya sun gano maganin da yake kashe cutar a cikin awa 48

Masana kimiyya a kasar Australia sunce sun gano wani magani da yake kashe cutar acikin awa 48, kamar yadda jaridar daily mail ta rawaito.

Maganin mai suna ivermectin, asali Ana amfani dashi wajen maganin kwarkwatar kai ne, kuma akwai shi a KO Ina a fadin duniya.
Masu bincike a jami'ar monash sun gano cewa shan kwayar maganin na ivermectin yana iya kashe kwayar cutar ta corona daga jikin kwayar halittar Dan Adam.

Se dai har yanzu ba'a yi gwajin kwayar maganin a jikin Dan Adam ba.
Masana kimiyyar sunce Abu na gaba shine gano yadda za'ai amfani dashi ga dan Adam wajen maganin cutar ta corona

Monday, April 6, 2020

Shin da gaske ne shan ruwan dumi ko yin sirace da ruwan zafi na maganin coronavirus?

Shin da gaske ne shan ruwan dumi ko yin sirace da ruwan zafi na maganin coronavirus?

Dakta Nasir Sani-Gwarzo wani fitacce kan harkar lafiya a Najeriya, ya ce yin sirace da ruwan zafi ba ya hana kamuwa da coronavirus amma zai iya taimakawa wajen jika makogwaro.

"Ita coronavirus cuta ce da take yaduwa ta hanci ko baki sai ta gangara makogwaro inda za tai ta hayayyafa har ta shiga huhu" a cewarsa.

Dakta Sani-Gwarzo ya ce idan ana yawan yin sirace, makogwaro zai zama a wanke ba tare da wata majina ba kuma wannan na iya taimakawa wajen hana cutar yaduwa, amma yin siracen ba ya maganin cutar.

Haka kuma shan ruwan dumi na taimakawa makogwaro wajen tsaftace shi da wanke shi yadda ya kamata ko da mutum ba ya dauke da wata cuta, amma Dakta Sani-Gwarzo ya ce ''wannan ba shi zai hana kamuwa da cutar ba kuma ba zai yi maganin cutar ba ga wanda ya kamu"

Saturday, March 28, 2020

Yanzu Yanzu: An gano Gwamnan Kaduna El-rufai na dauke da cutar Corona

Shafin kafar Sadarwa na twitter na matar Gwamanan be yabbana haka da yammacin nan, tace tini Gwamnan ya killace kansa duk da cewa be Fara nuna wata alama ta mash cutar ba.
Ta Bukaci Alumma da su yi masa adduar samun lafiya.

Thursday, March 26, 2020

An sake samun mai dauke da cutar Corona virus a jihar Bauchi.


Kwamishinan lafiya na Jihar Bauchi Dr Aliyu Mohammad Maigoro ne bayyana hakan ga manema labarai a yau Alhamis.
Wannan daya ne daga cikin mutane 48 wadanda suka fi shiga hadarin kamuwa da cutar sakamakon yin mu'amala da mutum na farko mai dauke da cutar a jihar, wato gwamnan jihar Bala Mohammad.
Kwamishinan bai Bayyana ko wanene ( ko kuma ko wacece) mai dauke da cutar ba, sai da bayyana cewa wani Abokin ( Ko kuma kawar) Gwamnan Bauchi Bala Mohammad ne, kuma dan ( KO yar) shekara sittin da biyu ce (ne).
Yace tini a killace me dauke da cutar, kuma Ana bashi kulawa, sannan yaja hankalin mutanen jahar da su cigaba da bawa Gwamnatin jihar hadin kai wajen yaki da cutar.

Tuesday, March 24, 2020

CUTAR CORONA: SHIN DA GASKE SINADARIN CHLOROQUINE YANA MAGANINTA?


Tun bayan da aka samu labarin rahoto na farko na billar cutar corona a kasar man mutane da yawa suka Shiva cikin halin dimuwa DA tashin hankali, karin samun rahottanin bullar cutar a wasu sassa na kasar bayan jihar Lagos da cutar ta Fara bulla a sanadiyar wani mutumin kasar Italiya ya Kara ta'azzara tsoro DA fargaba DA ke cikin zukatan mutane.

 kwatsam kuma sai aka samu labarin dake nuna cewa sinadarin chloroquine yana maganin wannan cuta, Tun daga nan ake ta samun turruruwar mutane a shagunan saida magunguna domain siyan wannan magani da niyyar yin Riga kafi.
Abinda ya kamata mutane su fahimta shine illar daukar matakin kare ba tare da samun sahalewa daga masana lafiya ba a wadansu lokutan yakan fi ita  cutar da ake kokarin kare kai daga ita din, Dan haka duk da cewa an tabbatar da cewa chloroquine yana maganin kwayar cutar corona hakan ba wai yana nufin cewa za'a iya amfani dashi wajen yin rigakafi bane.

Riga kafin cutar corona, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya take ta  kara jaddaddawa sune kamar haka:

1- Yawan wanke hannewa da ruwa da sabulu
2- Yin amfani da sinadarin wanke hannu mai sinadarin kashe kwayoyin cuta ( Hand sanitizer)
3-  Kauracewa gurin me cunkosan mutane
4- Yin baya-baya da mutanen da aka suna tari KO attishawa
5- Yin kasan cewa cikin tsafta a ko da yaushe.

Shi kuwa maganin chloroquine wadanda aka tabbatar da cewa sun kamu da wannan cuta ne kadai zai yiwa amfani, kuma masana kiwon lafiya su suka San irin yadda za'a yi amfani dashi don maganin wannan cuta.
Shan maganin chloroquine fiye da kima Nada wadansu hadarrarrrukan da zai iya haifarwa, kamar makantar da mutum da sauransu, dan haka yakamata mutane su kiyayye.